Har yanzu ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

Har yanzu ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

Daga karshe, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yace bayyana cewa babu makawa zai fice daga jam'iyyar APC.

Gwamnan ya shaida wa 'yan kungiyar kwararen na kabilar Tibi na 'OnTiv' a babban birnin tarayya Abuja cewa babu abinda zai sa ya cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC.

Sai da gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu bai fice daga jam'iyyar APC ba, bayan ya gana da shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, inda a lokacin yace akwai yiwuwar za'ayi sulhu.

Ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

Ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

DUBA WANNAN: Shugabanin kungiyar masoya Buhari sun kai ziyara fadar gwamnati, kalli hotuna

Amma kuma lokacin da ya karbi bakinsa a gidan gwamnatin Benue dake Abuja, gwamnan yace : "Ina son in tabbatar ma mutanen Benue cewa babu gudu-babu-ja-da baya kan batun ficewa na daga jam'iyyar APC."

Ya kara da cewa nan da wasu makonni kalilan idan lokaci ya yi, zan shaida wa mutane matakin da na dauka.

A lokacin da yake tsokaci kan kalaman da jam'iyyar APC reshen Benue ta fadi na cewa shine ya bawa kansa jan kati bayan jam'iyyar ta tuntube shi game da wasu lamaran shugabanci, Ortom yace mutum daya ne kawai ke juya jam'iyyar.

Ortom ya kuma ce a lokacin da jam'iyyar ta gudanar da taron gangami na jihar, mahukunta jam'iyyar sun nemi tsayar dashi a matsayin dan takara ba tare da hammaya ba amma sai yaki amincewa saboda yana daraja demokradiya.

Ya bukaci a bawa mutanen dake sha'awar takara dashi su fito kana a gwabza a zaben fidda gwani saboda yana son kafa jam'iyyar kan turbar demokradiya na gaskiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel