Matashi dan shekara 19 ya kashe budurwarsa sannan ya jefar da gawarta akan hanya

Matashi dan shekara 19 ya kashe budurwarsa sannan ya jefar da gawarta akan hanya

Wani matashi dan shekara 19 mai suna Junior Omo Shaba ya kashe budurwarsa sannan ya bar gawarta akan hanya.

Lamarin a faru ne a gida mai lamba 2 unguwar Akugbe, Ogida karamar hukumar Egor.

An tattaro cewa an soki marigayiyar, Matilda Odiri, wacce keda shekaru 18 a duniya da wuka a cikin dakin saurayin nata dokacin wani sabani.

Marigayiyar ta je gidan saurayin nata domin kwana lokacin da aka soke tad a wuka a saman nononta na dama.

Matashi dan shekara 19 ya kashe budurwarsa sannan ya jefar da gawarta akan hanya

Matashi dan shekara 19 ya kashe budurwarsa sannan ya jefar da gawarta akan hanya

Idanun shaida sunce an soki buduwar ne da misalin karfe 11 na dare bayan saurian ya zarge ta da mu’amala da sauran mata.

An rahoto cewa saurayin ya jefar da gawarta akan hanya bayan kasheta domin kare kansa daga laifin da ya aikata.

An bayana cewa ya tsere lokacin da mahaifinsa ya kira yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

Majiyoyin yan sanda sun bayyana cewa mai laifin na hannun hukumar binciken masu laifi na jiha a yanzu haka.

Majiyar yan sandan ta bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa shine ya kashe masoyiyar tasa sannan ya jefar da gawarta a hanya bayan wani sabani ya shiga tsakaninsu da daddare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel