Hukumar Kastam reshen Apapa ta samar da N176.7bn na kudaden shiga cikin watanni shida

Hukumar Kastam reshen Apapa ta samar da N176.7bn na kudaden shiga cikin watanni shida

Hukumar kastam reshen Apapa dake jihar Legas, ta samar da kudaden shiga na Naira biliyan 176.7 cikin watanni shidan da suka gabata, wanda ya kasance kari akan adadin Naira biliyan 165.74 da ta samar cikin wannan tsawon lokuta a shekarar 2017 da ta gabata.

Kakakin hukumar, Mrs Nkeiruka Nwala, ita ta bayyana hakan a birnin Legas yayin ganawa da manema labarai kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito a ranar Juma'ar da ta gabata.

Nwala take cewa, an samu karuwar adadin kudaden shiga sakamakon kaddamar da wata sabuwar fasahar zamani dake taimakawa wajen tabbatar da gaskiya da amincin samar da kudaden shiga wajen shigowar kayayyaki cikin kasar nan.

Hukumar Kastam reshen Apapa ta samar da N176.7bn na kudaden shiga cikin watanni shida

Hukumar Kastam reshen Apapa ta samar da N176.7bn na kudaden shiga cikin watanni shida

Ta ci gaba da cewa, duk da kasancewar nasarar hukumar, an samu tangarda da nakasun kari akan wannan adadin kudi a sakamakon gyaran hanya da ya janyo rashin fitar kayayyaki cikin gaggawa daga tashar ta jiragen ruwa.

A cewar Nwala, wannan reshe na hukumar yana daya daga cikin wadanda fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zaba domin saukaka harkokin su na gudanar da ayyukan fasakauri.

KARANTA KUMA: Marasa Martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP - Oshiomhole

A yayin haka Nwala ta yi fashin baki da cewa, shugaban reshen hukumar Kwanturola Jibril Musa, tuni ya dabbaka umarnin gwamnatin tarayya da ya sanya hukumar ta taki wannan babbar nasara.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar za ta ci gaba da jajircewa domin cimma manufar da sanya a gaba wajen samar da Naira biliyan 426 a wannan shekara ta 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel