INEC ta saki tsarin lokacin zabuka 4 da zata gudanar

INEC ta saki tsarin lokacin zabuka 4 da zata gudanar

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki tsarin lokacin gudanar da shirye-shiryen zabuka hudu da zata gudanar.

Hukumar a ranar 19 ga watan Yuli, ta sanar da cewa a ranar 11 ga watan Agusta zata gudanar da zabuka hudu domin cike gurabe a yankunan Katsina ta Arewa da Bauchi ta Kudu a Katsina da kuma Bauchi. Haka kuma zata cike na mazabar Lokoja/Kogi/Koton Karfe a jihar Kogi da Obudu a jihar Cross River.

An yanke wannan hukunci ne bayan sanar da guraben aiki da majalisar dokoki na kasa da kuma majalisar dokokin jihar Cross River suka yi.

Sakamakon haka, hukumar ta amince da tsarin lokaci da kuma shirya lokacin aiwatar da zabukan.

INEC ta saki tsarin lokacin zabuka 4 da zata gudanar

INEC ta saki tsarin lokacin zabuka 4 da zata gudanar

Bisa ga tsarin lokacinda sakataren hukumar ta sanya hannu, Augusta Ogakwu, ranar karshe na gudanar da zaben fidda gwani ga jam’iyyun siyasa zai kama ranar 25 ga watan Yuli, yayinda ya zama dole a gabatar da fam ga hedkwatar INEC a ranar 27 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Muna tsimayin Kwankwaso a PDP kwanan nan – El-Doguwa

Bayan haka sunayen yan takara da sunayen da aka gabatar da jawaban tawagar jam’iyya zai kammala a ranar 3 ga watan Agusta.

Bisa ga tsarin lokacin, ana sanya ran kawo karshen gangamin zabe a ranar 9 ga watan Agusta domin bayar da hanyar zabukan bayan kwanaki biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel