Dalilin da yasa ake yawan samun afkuwar hatsari a titin Badagry zuwa Seme - Hukumar FRSC

Dalilin da yasa ake yawan samun afkuwar hatsari a titin Badagry zuwa Seme - Hukumar FRSC

Hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC reshen Badagry tace satar hanya da direbobi keyi yana daga cikin dalilan dake janyo haddura a babban titin Badagry-Seme.

Kwamandan yankin, Mr Fatai Bakare, yace sau da yawa ana kama direbobi suna biyo hanyar da ba tasu ba a titunan Badagry.

"Satar hanya da wasu direbobi keyi shine babban abinda yafi janyo haddura kuma masu abin hawa da yawa suna aikata hakan.

"Badagry gari ce dake kan iyaka saboda haka ana samun hada-hadan motocci sosai. Mafi yawancinsu kuma basu tuki cikin natsuwa wanda hakan ke janyo haddura a yankin," inji Kwamandan.

Abinda ke haifar da haddari a babban titin Badagry/Seme - Hukumar FRSC

Abinda ke haifar da haddari a babban titin Badagry/Seme - Hukumar FRSC

DUBA WANNAN: Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Bakare ya cigaba da cewa baya ga satar hanya, daukan kaya fiye da kima shima yana daga cikin laifukan da ake yawan samun masu ababen hawa na aikatawa, duk da irin wayar da kan mutane da direbobi da hukumar keyi.

Kazalika, yace hukumar ta samar wa jami'anta kayayakin aiki wanda zasu taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin sauki.

Cikin kayayakin aikin da aka samar wa jami'an sun hada da na'urar 'Aquilizer' ta auna numfashin direba saboda a gano ko ya sha barasa.

"Amfani da Aquilizer ya kawo ragowar adadin direbobin da ke shan giya lokacin da suke tuki kuma a kullum muna shawarta direbobi su guji shan barasa muddin za suyi tuki." inji Bakare.

Kwamandan ya shawarci direbobi su rika duba tayoyinsu domin su tabbatar akwai iska isashe a ciki kafin su fara amfani da motocin a kowanne lokacin da za suyi tafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel