Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

A ranar Juma’a, 20 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yanke shawarar sanar da kudirinsa na sake takara da wuri a watan Afrilu domin ya kwantar da hankula.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda a karbi bakuncin mambobin kungiyar magoya bayansa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya gode mambobin kungiyar kan yadda suke tare das hi tsawon shekaru da dama ba tare da sun samu komai ba.

Buhari ya bayyana cewa kasancewar ya nemi takara sau hudu kafin yayi nasara, yana sane da abubuwan dake faruwa a mazabu daban-daban.

Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

Ya kara da cewa faduwa da yayi sau uku a baya ya kasance saboda wasu mutane dake zaune a wani waje suna rubuta sakamakon zabe sannan su mukaci masu fafutuka su je kotu.

Yace yana mamakin ta yadda dan siyasan dake tunanin abincin da zai ci a gaba zai samu kudin biyan lauyoyi.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

Da yake yabama samar da fasaha wanda ya taimaka wajen nasararsa a zaben da ya gabata, shugaban kasar yayi kira da kungiyar da ta karfafawa yan Najeriya gwiwar karban katin zabensu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel