Marasa Martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP - Oshiomhole

Marasa Martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP - Oshiomhole

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, a ranar Alhamis din da ta gabata ne jam'iyyar APC ta gudanar da zaman dinke baraka da sulhu a tsakanin mambobin ta masu yunkurin sauye sheka daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Cikin babban birnin kasar nan shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole a ranar da ta gabata ya gana da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, wanda ke ikirarin tuni jam'iyyar ta APC reshen jihar sa ta yi ma sa kora da hali.

A baya dai Ortom yana daya daga cikin gwamnonin da ake san ran zai sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP. Sai dai shugaban jam'iyyar na kasa ya bayyana cewa, mambobin su marasa martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Marasa Martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP - Oshiomhole

Marasa Martaba ne kadai zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP - Oshiomhole

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da wasu shugabanni da gwamnonin jam'iyyar tare da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da wasu gwamnoni uku na jam'iyyar APC suka gudanar da taron tabbatar da nasarar sauya sheka a birnin Ilorin na jihar Kwara.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnonin sun hadar da; Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato da kuma Samuel Ortom na jihar Benuwe.

KARANTA KUMA: Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale na jam'iyyar APC - Atiku

Sai dai gwamnan na jihar Kwara ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu yana nan a jam'iyyar ta APC bayan ganawar su da shugaban ta.

Kazalika Oshiomhole ya bayyana gwamna Ortom a matsayin mutum mai martaba da zai sake gyara zaman sa cikin jam'iyyar da ya shigo tun shekaru uku da rabi da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar wakilai reshen jam'iyyar APC ta shiga cikin taro na gaggawa yayin da wasu jiga-jigan mabobin ta suka sauya sheka, sai dai shugaba na majalisar Femi Gbajabiamila ya ce ba wani abun tayar da hankali ba ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel