Muna tsimayin Kwankwaso a PDP kwanan nan – El-Doguwa

Muna tsimayin Kwankwaso a PDP kwanan nan – El-Doguwa

Shugaban jam’iyyar Democratic Party (PDP) a jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibrial Doguwa ya bayyana cewa jam’iyyar na tsimayin Sanata Rabi’u Kwankwaso kwanan nan.

Doguwa a wata hira da yayi da majiyarmu ta Daily Trust a jiya, ya bayyana cewa har yanzu suna tattaunawa kan shawo kan tsohon gwamnan kan ya bar APC sannan ya dawo tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP gabannin zaben 2019.

Muna tsimayin Kwankwaso a PDP kwanan nan – El-Doguwa

Muna tsimayin Kwankwaso a PDP kwanan nan – El-Doguwa

Doguwa yayi bayanin cewa duk da cewar ana tattaunawar ne a matakin kasa, sai dai jam’iyyar reshen jihar Kano ta kammala duk shirye-shiryenta domin tarban Sanata Kwankwaso.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Mambobin majalisar wakilai masu goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayar da cikakken bayanin abunda suka tattauna da shugaban kasar lokacin da suka yi ganawar sirri a yammacin ranar Alhamis.

Magoya bayan shugaban kasar sun gana das hi a dakin taro na ofishin uwargidan shugaban kasar. Sun samu jagorancin abokan aikinsu biyu, Musa Sarkin-Adar da Abdulmumin Jibrin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel