Jam’iyyar PDP ta fara shirye-shiryen lashe zabe mai zuwa

Jam’iyyar PDP ta fara shirye-shiryen lashe zabe mai zuwa

- Jam’iyyar PDP za ta fara gudanar da zaben fitar da gwani kwanan nan

- Ana sa ran a tsaida ‘Dan takarar da zai gwabza da Buhari a zaben 2019

Mun fara jin kishin-kishin din cewa babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta fara shirin gudanar da zaben fitar da gwani na zabe mai zuwa. Jaridar The Punch ce ta bayyana wannan labari ba da dadewa ba.

Jam’iyyar PDP ta fara shirye-shiryen lashe zabe mai zuwa

PDP na daf da gudanar da zaben fitar gwani na zaben 2019

Jam’iyyar adawar za ta zabi ‘Dan takarar da zai rike mata tuta a zaben Shugaban kasa a 2019 domin ya kara da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Jam’iyyar APC wanda bisa dukkan alamu zai sake neman takarar Shugaban kasa.

Ana sa rai a Ranar 30 ga Watan Satumba a gudanar da zaben tsaida ‘Dan takarar PDP na zabe mai zuwa a shekarar badi. Za kuma a fitar da masu neman takarar Gwamna ne a Ranar 21 ga Watan na Satumba mai zuwa idan Allah ya kai mu.

KU KARANTA: PDP za ta lashe zaben 2019 inji tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar

Majiyar ta bayyana cewa za a bada tikitin takarar Sanata ne a Ranar 18 ga Watan Satumba, hakan zai kama ne bayan kwanaki 4 da yin zaben ‘Yan Majalisun Tarayya. Za kuma ayi zaben fitar da gwanin ‘Yan Majalisar dokoki ne a Ranar 8.

A karshen watan gobe watau Agusta ne za a zabi wadanda za su tantance masu neman takara a Jam’iyyar. A tsakiyar watan na gobe ne ake tunani masu neman kujerun takara za su saye fam domin a gwabza da su a zaben da za ayi a 2019.

Kun ji labari cewa daga cikin zaben da APC ta sha kashi bayan ta hau mulki akwai wanda aka tika Jam’iyyar da kasa a wani zabe da aka yi a Jihar Oyo. Wani Matasahi daga PDP ne ya doke APC a zaben Majalisar dokoki a inda APC ta ke da karfi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel