Sarah Onyango Obama: Dangin Iyayen Obama da ta ke addinin Musulunci

Sarah Onyango Obama: Dangin Iyayen Obama da ta ke addinin Musulunci

- Kakannin tsohon Shugaban Amurka Obama Musulmai ne

- Sarah Ogwel Obama har yau Musulma ce da ke kasar Kenya

- Sai dai shi Barack Hussein Obama Kirista ne ba Musulmi ba

Sarah Onyango Obama wata Kakar tsohon Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ce da ke zaune a Kasar Kenya. A kan kira wannan tsohuwa mai shekaru 86 a Duniya da Sarah Ogwel Obama ko kuma Sarah Hussein Obama a wani lokacin.

Sarah Onyango Obama: Dangin Iyayen Obama da ta ke addinin Musulunci

Misis Sarah Onyango Obama mai dakin Kakar Obama ce

Wannan Baiwar Allah da har yanzu tana raye a Kasr Kenya, Kishiyar Kakar Obama ce. Barack Obama wanda asalin Iyayen su Mutanen Kasar Kenya ne ya zama Bakin farko da ya mulki Kasar Amurka inda ya kammala wa’adin sa a farkon 2017.

Miss Onyango Obama Malamar Makaranta ce asalin ta kuma ta kan taimakawa Marasa karfi a Yankin ta. Sarah Ogwel Obama tana zaune ne a a Garin Nyan’oma Kogela wanda ke kusa da babban Birnin Kisumu da ke Yammacin Kasar Kenya.

KU KARANTA: Ruwa yayi awon gaba da wata 'yar karamar yarinya

Tsohon Shugaban Kasar Amurkan Obama ya kan kira ta ne da Goggo Sarah watau Sarah Granny. Sai dai ita ba ta iya Ingilishi ba don haka sai an nemi tafinta idan za ta zanta da jikan ta Obama. Sarah Obama ta na jin yaren Luo ne na mutanen Kenya.

A 2008 lokacin Obama na neman mulki, 'Yan adawa sun yi ta kokarin nunawa Duniya cewa shi Musulmi ne 'Dan Afrika domin kuwa Kakannin sa Musulmai be. Sarah Obama dai har yau ta na yin sallah da sauran ibada na addinin Musulunci.

A Najeriya kuma kun ji labari cewa wata Kungiya mai suna ODI Oduduwa Development Initiatives sun fito sun kare Ministar kudin Najeriya watau Misis Kemi Adeosun wanda ake zargin ta kirkiri shaidar bogi na shirin bautar kasa watau NYSC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel