Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

Kungiyar magoya bayan Atiku, sun zargi gwamnatin tarayya da shirin danganta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kashe-kashen makiyaya a yankunan kasar.

Babban sakataren kungiyar, Awwal Tahir, yayi zargin cewa manyan yan siyasa a fadar shugaban kasa na shirin danganta Atiku da kisan kiyashin da ake yi a kasar.

A wata sanarwa da suki a jiya, yayi zargin cewa: “A ranar 25 ga watan Yuni, 2018, mun samu rahoton kwararru daga jami’in hukumar tsaro na kwararru, cewa wasu manyan yan siyasa a fadar shugaban kasa na kokarin danganta hare-haren makiyaya a fadin kasar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

“Don haka, an gabatar mana da takardu dauke da irin wannan makirci daga jami’in wani hukumar tsaro a makon day a gabata.”

Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

Kungiyar magoya bayan Atiku sun yi zargin cewa ana shirya makirci don danganta Atiku da hare-haren makiyaya

Kwanan nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu yan siyasa na da hannu a kashe-kashen kasar. Koda da dai bai ambaci sunaye ba.

KU KARANTA KUMA: Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC

Atiku dai na hararar tikitin takarar shugaban kasa a lemar am’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin karawa da shugaba Buhari a zaben shekara mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel