Sanatan PDP ya bada shawarar a rika zabe da wayar salula domin hana magudi

Sanatan PDP ya bada shawarar a rika zabe da wayar salula domin hana magudi

- Sanata Ben Bruce ya nemi a rika zabe ta hanyar aika sako a waya

- ‘Dan Majalisar yace wannan dai zai yi matukar rage magudin zabe

- Ana zargin cewa mutane sun rika saida kuri’un su a zaben Ekiti

Dazu mu ka ji labari cewa wani ‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Yankin Bayelsa Ben Murray-Bruce yana nema a rika amfani da wayar salula wajen yin zabe nan gaba a Najeriya.

Sanatan PDP ya bada shawarar a rika zabe da wayar salula domin hana magudi

Ben Murray Bruce na kira a rika zabe ta hanyar salula

Sanata Ben Murray Bruce yana ganin zai yi kyau mutane su rika zabe daga gidajen su ba sai an je ko ina ba. Sanatan ya nuna cewa kusan kowa yana da waya a Kasar domin akwai wayoyin salula fiye da miliyan 100 a Najeriya.

KU KARANTA: Wasu sun budawa Sanata Dino Melaye wuta

A dalilin haka ne ‘Dan Majalisar ya nemi a rika yin zabe ta hanyar aika sako daga wayar ba tare da shan wahala a layin zabe ba. A cewar Sanatan, Hukumar sadarwa ta kasa watau NCC tayi kowa rajista don haka ta san lambar kowa.

Tun da Gwamnatin Tarayya tana da suna da hoto da kuma lambar kowani mai waya a Kasar, ‘Dan Majalisar da ke karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP yace yin haka zai rage magudin da ake tafkawa wajen sayen kuri’u a lokacin zabe.

A zaben da aka yi kwanan nan a Ekiti, masu lura da zaben sun yarda da abin da Gwamna Ayo Fayose ya fada. Turawa sun ce an yi amfani da sayen kuri’u wajen murde zaben. Kungiyoyin na kasar waje sun ce akwai sauran gyara a zaben Gwamnan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel