Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari

Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari

- An kama wani gardi sanye da hijabi da niqabi a wata tashan jirgin kasa dake Dubai

- Bayan an kama shi, mutumin ya fadawa 'yan sanda cewa ya yi bata kamar ne saboda ya bi sahun matarsa da yake zargin zata wajen saurayinta a Dubai

- Tuni an gurfana dashi gaban alkali a kotu kuma aka ci shi tarar Dirhami 2,000 wanda ya yi dai-dai da N196,000

Masoya ko ma'aurata su kanyi abubuwan mamaki a lokutan da suke zargin abokan zamansu na cin amanarsu. Wasu kan dauki hayar masu binciken sirri na musamman, yayin da wasu kuma suna daukan dawainiyar gudanar da binciken ne da kansu kai kace jami'an yan sanda ne.

Hakan ne ta faru da wanni magidanci da jami'an tsaro suka kama a tashan jirgin kasa na Dubai. Rahottani da muka samu sunce mutumin baiyi nasarar shiga tashan jirgin kasar ba saboda 'yan sanda sun gano shi.

Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari

Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari

DUBA WANNAN: Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Mutumin ya amsa cewa tabbas ya yi shiga irin ta mata inda ya sanya burgujejiyar hijabi da nikabi har ma da safar hannu inda yace yana bin sahun matarsa ne kamar yadda 24 ta ruwaito.

Yace ya saurari lokacin da take magana da masoyinta kuma suka yi shirin zasu hadu a tashan Al Fahidi dake Dubai.

Magidancin wanda manajan ne a wata kamfani ya shaidawa 'yan sanda cewa ya sayo tufafin matan ne bayan zargin da yake yiwa matarsa ya tsananta. Ya taso daga wajen aiki sai ya tsaya a motarsa ya canja tufafinsa ya yi shigar matan.

Tuni da 'yan sandan Dubai sun damke shi kuma an ci shi tarar zunzurutun kudi Dirhami 2,000 wanda a kudin Najeriya ya kai misalin N196,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel