Tsautsayi: Jirgin kasa ya niqe motar bas , har an rasa rayuka a jihar Ikko

Tsautsayi: Jirgin kasa ya niqe motar bas , har an rasa rayuka a jihar Ikko

- A kalla mutane biyu sun rasa rayukan su inda daya ya jikkata

- Jirgin kasan yayi daga-daga da wadanda suka rasun, yayinda wadanda suka tsira kuma suka rasa wasu sassa na jikinsu

- Zama a saman jirgin kasa yayinda yake tafiya nada matukar hatsari ya kamata mutane su dinga Sanin darajar rayukan su

Tsautsayi: Jirgin kasa ya niqe motar bas , har an rasa rayuka a jihar Ikko

Tsautsayi: Jirgin kasa ya niqe motar bas , har an rasa rayuka a jihar Ikko

A kalla mutane Biyu ne suka rasa rayukan su daya ya jikkata bayan wani jirgin kasa ya tura wata mota kirar Bus.

Hatsarin ya afkune a ranar Juma'a da safe a Pen cinema Agege jahar Legas.

Wadanda suka rasun dai suna zaune ne akan saman jirgin kasan lokacin da suka hangi motar daga can nesa.

Wadanda abun ya faru a gaban su sunce wadanda suka rasun dai sun fado ne a kan hanyar jirgin su kuma wadanda suka fada kan motar sun rasa wasu sassa na jikinsu.

Motar dai ta kama da wuta yayin da yan kallo suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibiti na Orile dake Agege.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari na neman Saraki ya yafe shi gabanin 2019

Janar managa na LASEMA Adesina Tiamiyu ya tabbatar da afkuwar hatsarin yace a halin yanzu an dauke motar a wajen:

'Munsha fadawa mazauna wajen dasu dena ajjiye abubuwa a wajen, sannan zama a saman jirgi a yayin da yake tafiya nada matukar hatsari, ya kamata mutane su dinga Sanin darajar rayukan su'.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel