Hukumar 'yan sanda ta aika sammaci ga Dino Melaye bayan yayi zargin wai suna neman ransa

Hukumar 'yan sanda ta aika sammaci ga Dino Melaye bayan yayi zargin wai suna neman ransa

Hukumar Yan sanda reshen jihar Legas ta gayyaci Sanata Dino Melaye, aya bayyana gaban sashin binciken manyan laifuka a hukumar (SCIID) sakamakon bude wuta da masu tsaronsa su kayi ga wata tawagar yan sanda yayin da suke sintiri.

Wani jami'in dan sanda mai mukamin Saja ya samu rauni sakamakon harbin da masu tsaron Dino su kayi amma yanzu yana asibiti yana samun sauki.

A cewar wata sanarwa data fito daga hannun Kakakin hukumar na Legas, DSP, William Ovye Aya, yace ikirarin da Dino Melaye ya yi na cewa 'yan sandan sun bude masa wuta ba gaskiya bane.

Hukumar 'yan sanda ta aika sammaci ga Dino Melaye bayan yayi zargin wai suna neman ransa

Hukumar 'yan sanda ta aika sammaci ga Dino Melaye bayan yayi zargin wai suna neman ransa

DUBA WANNAN: Wata mata ta kashe kanta bayan ta gano cewar mijinta ba saurayi bane

Hasali ma abinda ya faru shine, masu tsaron Sanata Dino Melaye ne suka fara bude wa jami'an yan sandan wuta, sannan 'yan sandan suka mayar da martani.

A bayanin da ya yi a shafinsa na Instagram, Melaye bai fadi cewa anyi musayar wuta ba. Ya dai yi ikirarin cewa anyi kokarin tsare shi ta hanyar amfani da wata babban mota a aka ajiye a gadar yayin da yake hanyarsa ta zuwa kaddamar da wasu ayyuka a Gabashin Yagba.

A shafinsa na Twitter kuma, Sanata Dino Melaye, ya yi ikirarin cewa anyi barazanar halaka shi ne a hanyarsa ta zuwa ziyarar jiharsa ta Kogi.

Ya yi ikirarin cewa yan sanda da yan sandan SARS sun harba harsashi sama da 20 a gareshi yayin da yake cikin babbar motarsa kirar Jeep.

Saidai rahoton da hukumar Yan sandan ta bayar ya sha ban-ban da abinda Sanatan ya fadi.

Sunce jami'an yan sandan suna gudanar da sintiri ne da aikinsu kamar yadda suka saba a hanyar Aiyetoro Gbede-Mopa.

Hukumar Yan sandan ta umurci Dino Melaye da masu tsaronsa su gabatar da kansu a ofishin SCIID dake Lokoja domin amsa tambayoyi game da lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel