Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC

Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC

Mambobin majalisar wakilai masu goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayar da cikakken bayanin abunda suka tattauna da shugaban kasar lokacin da suka yi ganawar sirri a yammacin ranar Alhamis.

Magoya bayan shugaban kasar sun gana das hi a dakin taro na ofishin uwargidan shugaban kasar.

Sun samu jagorancin abokan aikinsu biyu, Musa Sarkin-Adar da Abdulmumin Jibrin.

Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC

Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC

Da yake Magana da manema bayanai na majalisa bayan tattaunawar, Mista Sarkin-Adar yace ganawar “ya lura da abubuwan dake tafiya a cikin kasar da kuma jam’iyyun siyasa daban-daban saboda zabe na kara gabatowa.”

KU KARANTA KUMA: Yan kungiyar R-APC na majalisar wakilai sun dage sauya shekarsu zuwa mako mai zuwa

Ya ce a matsayin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a majalisar dokoki, suna ganin ya kamata su je su zanta da shugaba Buhari da shugaban jam’iyyar na kasa domin magance lamuran da mambobin kasar ke korafi akai a fadin kasar.”

Mista Sarkin-Adar, mai wakiltan mazabar Goronyo/Gada na jihar Sokoto, yace sun je fadar shugaban kasa domin inganta zamantakewa tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel