Dalilin da yasa ba za mu iya sakin Dasuki ba – Ministan Shari’a, Malami

Dalilin da yasa ba za mu iya sakin Dasuki ba – Ministan Shari’a, Malami

- Babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, ya jaddada cewa ba zai yiwu a take hakkin dubunnan mutane dan mutum daya ba

- Ya tuhumci Dasuki da taimakawa wajen mutuwan akalla mutane 100,000 a Najeriya

- Ana sa ran cewa za’a saki Dasuki bayan alkali ya bada belinsa

Babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, gwamnatin tarayya da kwararan dalilai na rashin sakin tsohon NSA, Sambo Dasuki.

A wani hira da Malami ya gabatarwa Muryar Amurka (VOA) Hausa, ya ce za’a iya take hakkin Dasuki domin amfanin al’uman kasa.

Yace gwamnatin Buhari na bin umurnin kotu amma al’amarin Dasuki daban ne saboda ya shafi dukkanin kasa.

A cewarsa: "Abinda nike son ku sani game da doka da oda karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shine bin umurnin kotu wajibi ne,”

“Amma fa ku sani cewa anyi ittifaki a duniya gaba daya cewa idan rigima tsakanin mutane biyu ne, za’a bi umurni kai tsaye. Amma idan wanda ya shafi mutanen kasa gaba daya ne, ya kamata ku tuna cewa gwamnati ta mutane ce ba mutum daya ba.”

Maganan da muke shine wannan mutum ne wanda ya taimaka wajen mutuwar akalla mutane 100,000. Yanzu kuna cewa hakkin mutum daya ya fi na mutane 100,000 da suka rasa rayukansa.”?

A farkon makon nan, alkalin babban kotun tarayya dake zaune a Abuja ta rattaba hannu kan belin Sambo Dasuki bayan ya cika dukkan sharrudan belin. Lauyansa ya bayyana cewa idan suka kai takardan ofishin DSS, za'a sake Dasuki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel