Buhari zai sha kashi hannun Atiku a Zaben 2019 - PDP Adamawa

Buhari zai sha kashi hannun Atiku a Zaben 2019 - PDP Adamawa

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Adamawa, Tahir Shehu ya bayyana cewa, muddin aka tafi da al'amurra ta hanyar dace to kuwa ko shakka babbu tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, zai fatattaki shugaban kasa Muhammadu Buhari daga fadar sa a zaben badi.

A cewar Shehu, tsohon mataimakin shugaban kasar kadai ke da cikakkiyar cancanta tare da mashahuran makaman yakin da zai sanya ya fatattaki duk wani dan takara da jam'iyyar APC za ta tsayar a babban zabe na shekara mai gabatowa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata cikin birnin Yola yayin bayar da sanarwar kaddamar da shirye-shiryen shawagi na yakin neman zabe ga Atiku da jam'iyyar za ta gudanar a jihar Adamawa.

A yayin gabatar da jawabai ga manema labarai a shelkwatar jam'iyyar ta jihar, Tahiru ya bayyana dawowar Atiku jam'iyyar ta PDP a matsayin waiwaye da hausawa kan ce adon tafiya ne da ya kasance babban kamu ga jam'iyyar.

Buhari zai sha kashi hannun Atiku a Zaben 2019 - PDP Adamawa

Buhari zai sha kashi hannun Atiku a Zaben 2019 - PDP Adamawa

Legit.ng ta fahimci cewa, a shekarar da ta gabata ne tsohon Mataimakin shugaban kasar ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP inda a halin yanzu yake fafutikar neman tikitin takarar jam'iyyar domin lallasa shugaba Buhari a babban zabe mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Dalilin rashin tattalin Gwamnatin Jonathan duk da hauhawar Farashin Man Fetur - Ngozi

Kazalika Shehu ya kara da cewa, dawowar Wazirin Adamawa jam'iyyar kadai ya isa ya tabbatar da samun tushen zamanta a jihar Adamawa koda kuwa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa a shirye jam'iyyar sa ta PDP take wajen tunkarar duk wani kalubale da barazanar tuggu ta jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel