Ina cikin gwamnoni 7 da Buhari ke son hanawa zarcewa a 2019 - Inji wani gwamnan Arewa

Ina cikin gwamnoni 7 da Buhari ke son hanawa zarcewa a 2019 - Inji wani gwamnan Arewa

Gwamnan jihar Taraba dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan, Mista Darius Ishaku ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirya makarkashiyar hana shi tare da wasu gwamnoni 6 sake tsayawa takara a 2019.

Darius Ishaku ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar, garin Jalingo.

Ina cikin gwamnoni 7 da Buhari ke son hanawa zarcewa a 2019 - Inji wani gwamnan Arewa

Ina cikin gwamnoni 7 da Buhari ke son hanawa zarcewa a 2019 - Inji wani gwamnan Arewa

KU KARANTA: Kayatattun hotunan filayen da za'a buga gasar kofin duniya na Qatar

Legit.ng ta samu cewa sai dai gwamnan yaki ya bayyana sauran gwamnonin da Buhari ke shiryawa makarkashiyar sannan kuma ya ce shi da Allah ya dogara kuma yasan ba bu mai iya hanashi.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya da cewa su burin su kawai su lashe zabe ba wai su gudanar da sahihin shugabanci ba.

Jega ya bayyana cewa wannan babbar matsalar ta su idan har aka duba itace ummul abasin dukkan koma bayan da kasar ke fama da ita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel