Zabukan 2019: Jami'an tsaro sun bukaci kashe Naira miliyan 317 don sayen abincin dabbobi

Zabukan 2019: Jami'an tsaro sun bukaci kashe Naira miliyan 317 don sayen abincin dabbobi

Ana cigaba da takaddama a tsakanin majalisar tarayyar Najeriya da kuma shugaban kasa game da wani sabon kasafin kudin da yakai don su amince masa na kudaden da hukumar zabe ke bukata don gudanar da zabukan 2019.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, a cikin sabon kasafin kudin, jami'an tsaron kasar da suka hada da 'yan sanda da kuma masu tsaron farar hula na Nigeria Security and Civil Defence Corps sunce suna bukatar zunzurutun kudi har Naira miliyan 317 don ciyar da dabbobin su abinci.

Zabukan 2019: Jami'an tsaro sun bukaci kashe Naira miliyan 317 don sayen abincin dabbobi

Zabukan 2019: Jami'an tsaro sun bukaci kashe Naira miliyan 317 don sayen abincin dabbobi

KU KARANTA: Allah ya yiwa tsohon sifeto janar na 'yan sanda rasuwa

Legit.ng dai ta samu cewa dabbobin da suka hada da karnuka da kuma dokuna, sun ne za'a siyawa abinci na musamman domin sa ido akan yadda za'a gudanar da zabukan a dukkan fadin kasar.

A wani labarin kuma, Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su yayin da kuma da yawa suka bace bat har yanzu ba'a gansu biyo bayan wani mummunan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai wa wasu matafiya akan hanyar Dikwa zuwa Ngala a jihar Borno.

Wani ganau ya shaidawa majiyar ta Daily trust a wayar tarho cewa akalla motoci 27 ne dauke da mutane da kayayyakin masarufi 'yan ta'addan suka tare suna harbi kafin daga bisani mutanen ciki su tsere.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel