Yan Majalisu zasu binciki Buhari kan zargin nuna son kai a nade naden mukamai

Yan Majalisu zasu binciki Buhari kan zargin nuna son kai a nade naden mukamai

A ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli ne majalisar dattawa a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta umarci wani kwamitin majalisa da ya binciki zargin da ake yi ma shugabn kasa Muhammadu na nuna son kai da wariya a nade naden mukaman da yake a yi a gwamnati.

Jaridar Leadrship ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu ya janyo hankalinta ga irin abinda ya bayyana a matsayin rashin aldalcin da Buhari ke yi a wajen nade nade, inda yace yafi mayar da hankali a wani yankin kasar nan.

KU KARANTA: Mutuwar Ibrahim Coomassie: Mun shiga cikin dimuwa matuka – Kungiyar Dattawan Arewa

Wannan korafi na Ekweremadu ya biyo bayan wata wasika da Buhari ya aika ma majlisar yana bukatar da ta tabbatar da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Tunde Lemo a matsayin shugaban hukumar kula da hanyoyin gwamnatin tarayya.

Kammala karanta wasikar Buhari daga bakin Saraki keda wuya, sai Ekweremadu ya yi caraf ya kama, yana babatu tare da yin nuna da kundin tsarin mulkin Najeriya da acewarsa ya bukaci duk nade naden da gwamnati za ta yi ta tabbata wani yanki na kasarnan bai rinyaje wani ba.

Sai dai Sanata Ahmad Lawan shugaban masu rinyaje ya yi watsi da wannan zargi na mataimakin shugaban majalisa, inda yac kafin yayi wannan magana ya kamata ya duba sauran nade naden da Buhari ya yi a baya a hukumomi daban daban.

Bayan sauraron cecekucen da ya biyo bayan wasikar da ya karanta, Sanata Saraki ya bayyana cewa za’a duba wannan korafi a matsayin ra’ayi ne na kashin kan wadanda suka bayyana shi, ba wai na majalisa ba, don haka ya umarci kwamitin majalisa mai kula da nade naden gwamnati ta binciki wannan zargi ya kawo masa rahoto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel