Anyi wa Ezekwesile tatas kan tsinuwar da tayi wa sabon jirgin saman Najeriya

Anyi wa Ezekwesile tatas kan tsinuwar da tayi wa sabon jirgin saman Najeriya

- Najeriya naso ta dawo da martabarta a idon duniya

- Anyi tofin ala-tsine kan Obi Ezekwesile

- Tsinuwa da fatan sharri tayi wa shirin na dawo da jirgin saman Najeriya

Anyi wa Ezekwesile caa kan tsinuwar da tayi wa sabon jirgin saman Najeriya

Anyi wa Ezekwesile caa kan tsinuwar da tayi wa sabon jirgin saman Najeriya

Tsohuwar ministar ilimi ta kasa, Obi Ezekwesile, tasha tofin ala-tsine, bayan da ta ce tana fata sabon jirgin samar Najeriya zai sha kasa, kamar yadda ta wallafa a shafin ta na tuwita. A cewarta, lallai wannan shiri ba zai yi nasaraba, kuma bata fatan ci gaban shirin.

A cewarta dai, wai barnar kudin talakawa ne kawai za'a y, kamar yadda aka yi a baya.

Wasu na ganin don gwamnatin nan bata kira ta bane take ta fushi da ita.

Masu bibiyar shafinta na tuwita, @obyezeks, na can suna maida mata da martani, kuma dukka kausasa masu jiyar da ita kunya.

Gwamnati tace babu ko sisi da za'a kashe wajen harkar jirgin. Jari ne na 'yan kasuwa, sai kashi biyar bisa dari na kudin suna da kasar zata bada haya.

DUBA WANNAN: Zaku sami karin bayani kan karin albashi a banan nan

A cewar majiyarmu dai, za'a kashe dala miliyan takwas a bana, sannan $300m a cikin shekaru 3 kafin a ara cin riba daga harkar, za'a samar da jirage 40 cikin shekaru biyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel