Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale na jam'iyyar APC - Atiku

Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale na jam'iyyar APC - Atiku

A yayin mayar da martani dangane da zargin shirye-shiryen gwamnatin jam'iyyar APC na gudanar da magudi a babban zaben kasa na 2019, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, jam'iyyar su ta adawa ta PDP a shirye take tsaf domin tunkarar wani kalubale ko barazana da za ta kunno kai a zaben.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Atiku ya ziyarci jihar Taraba ne domin neman goyon bayan al'umma tare da babban hadimin sa na yakin neman zabe, Gbenga Daniel, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Ogun.

Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale na jam'iyyar APC - Atiku

Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale na jam'iyyar APC - Atiku

Gwamnan jihar Darius Ishaku da mataimakin sa Haruna Manu, Kakakin majalisar dokoki na jihar, Abel Peter Diah, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Victo Bala da sauran mashahuran jiga-jigai sun tarbi tsohon mataimakin shugaban kasar a fadar gwamnatin jihar dake birnin Jalingo.

KARANTA KUMA: Rayukan Mutane 215 sun salwanta a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun cikin watanni shidda

Atiku wanda haifaffen jihar Adamawa ne ya bayyana cewa, jihar Taraba tamkar gida ce a wurinsa ta fuskar siyasa kasancewar riko da ta yi da jam'iyyar PDP tun a shekarar 1999 da ya tabbatar da amanar ta.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, muddin kuri'un al'ummar kasar nan suka tabbatar da nasarar sa a zaben 2019 to kuwa ya sha alwashin sauya fasalin ta domin cikar burika da muradin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel