Dalilin rashin tattalin Gwamnatin Jonathan duk da hauhawar Farashin Man Fetur - Ngozi

Dalilin rashin tattalin Gwamnatin Jonathan duk da hauhawar Farashin Man Fetur - Ngozi

Tsohuwar Ministan kudi ta Najeriya, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi fashin baki dangane da gazawar gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wajen tattalin dukiya duk da hauhawa da tsadar man Fetur a kasuwar duniya.

Dakta Iweala ta bayyana cewa, tsohuwar gwamnatin ta gaza tanadin dukiyar kasar nan sakamakon dagewar gwamnoni wajen kasafta ribar ta man fetur ga jihohin su.

A cewar Okonjo-Iweala, duk da kasancewar ta Ministan kudi tare da samun goyon bayan Jonathan da mataimakin sa, Namadi Sambo, sai da ta kai ruwa rana da gwamnonin jihohi da suka dage akan babu wani amfani tattalin dukiyar kasar nan duk da farashin man fetur yana $86 na kowace ganga guda.

Dalilin rashin tattalin Gwamnatin Jonathan duk da hauhawar Farashin Man Fetur - Ngozi Okonjo-Iweala

Dalilin rashin tattalin Gwamnatin Jonathan duk da hauhawar Farashin Man Fetur - Ngozi Okonjo-Iweala

Tsohuwar Ministan ta bayyana hakan ne cikin sabon littafin da ta wallafa a kwana-kwanan nan kan barazanar dake tattare da yakar cin hanci da rashawa mai taken “Fighting Corruption Is Dangerous: The Story Behind the Headlines.”

DUBA WANNAN: N5, 000 nake karba a duk harin kunar bakin wake da na dauki nauyin shirya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya gaji tsohuwar gwamnatin na ci gaba da zargin ta kan gazawar gwamnatin sa na cika alkawurran ta na yakin neman zabe sakamakon rashin tattalin dukiya daga bangaren gwamnatin da ta shude.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwar sa dangane da yadda kasar nan ke zaune cikin rashin kudi a sanadiyar gazawar gwamnatin baya na almubazzaranci da rashin tattalin dukiya duk da hauhawa da tsadar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Legit.ng da sanadin shafin jaridar The Punch ta fahimci cewa, wannan shine musabbabin da ya jefa kasar nan cikin masti na tattalin arziki a shekarar 2016 da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel