2019: 'Yan takarar APC 4 sun hade kai domin tunkarar Buhari a zaben fitar da gwani na jam'iyyar

2019: 'Yan takarar APC 4 sun hade kai domin tunkarar Buhari a zaben fitar da gwani na jam'iyyar

Wasu 'ya'yan APC dake neman jam'iyyar ta tsayar da su takarar shugabancin kasa sun garzaya wurin shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, da kukan su.

Hudu daga cikin 'yan takarar su 5 sun yi zargin ana fifita shugaba Buhari tare nuna kin amincewa da ayyana Buhari a matsayin dan takarar APC tun kafin a gudanar da zaben fitar da dan takara.

'Yan takarar hudu, Mista Adamu Garba, Dakta SKC Ogbonnia, Cif Udo Udeogaranya da Alhaji Mumakai Unagha, sun aike da takarda kokensu ga jaridar Vanguard.

2019: 'Yan takarar APC 4 sun hade kai domin tunkarar Buhari a zaben fitar da gwani na jam'iyyar

Buhari

Shugaba Buhari ne mutum ne cikon mutum na 5 dake son yiwa APC takara.

A ranar Litinin da ta gabata ne Oshiomhole ya bayyana cewar APC na iya watsi da duk mai son ta tsayar da shi takara saboda shugaba Buhari ne ya fara bayyana niyyar yiwa jam'iyyar takara.

DUBA WANNAN: 2019: Jarumin Fim ya ci alwashin lashe zaben gwamna a jihar sa

Saidai Dakta Ogbonnia ya shaidawa Vanguard cewar Oshiomhole na magana ne a kashin kansa amma ba da yawun jam'iyyar APC ba.

Kazalika, Adamu Garba ya bayyana cewar APC jam'iyyar siyasa ce da manufofinta bai kamata su saba da na dimokradiyya ba.

Shi kuwa Alhaji Unagha, dan asalin jihar Delta, a nasa martanin ya bayyana cewar kalaman Oshiomhole sun ci karo da kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel