Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa tsohon sifeto Janar na yan sandan Najeriya, Ibrahim Coomassie rasuwa
1 - tsawon mintuna
Da yammacin yau ne muka samu labarin cewa Allah ya yiwa tsohon sifeto Janar na yan sandan Najeriya, Ibrahim Coomassie rasuwa a mahaifar sa ta jihar Katsina bayan ya sha fama da gajeruwar rashin lafiya.
Shi dai Ibrahim Coomassie shi ne Sardaunan Katsina kuma garkuwan Hausa. Haka ma kuma shi ne shugaban kungiyar tattaunawa ta dattijan Arewa watau (Arewa Consultative Forum).
Asali: Legit.ng