Ba a tattauna maganar yadda za a raba kudade ga jihohi ba a taron FAAC

Ba a tattauna maganar yadda za a raba kudade ga jihohi ba a taron FAAC

Taron Majalisar Zartarwar Tattalin Arzikin Kasa da aka gudanar a yau Alhamis, 19 ga watan Yuli ya kasa shawo kan yadda za’a warware hanyar da za a kasafta kudaden da gwamnatin tarayya ke rabawa kanta da jihohi da kuma kananan hukumomi.

Premium Times ta rahoto cewa ba’a ma tattauna lamarin ba a taron wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

Da wadannan kudaden ne ake biyan albashin ma’aikata da sauran ayyukan yau da kullum a jihohi da kananan hukumomi har da tarayya baki daya da hakan yasa har yanzu wasu jihohin basu iya biyan albashin ma’aikatan su na watan Yuni ba.

Ba a tattauna maganar yadda za a raba kudade ga jihohi ba a taron FAAC

Ba a tattauna maganar yadda za a raba kudade ga jihohi ba a taron FAAC

Mataimakin shugaban kasa Farfsa Yemi Osinbajo ne jagoran wannan majalisa, inda a cikinta akwai gwamnonin jihohin kasar.

Saboda karancin kudade a aljihun jihohi tare da kasa samun kudade na watan Yuni da tarayya, akasarin jihohi har yau ba su biya albashin watan Yuni ba.

KU KARANTA KUMA: Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

Bayan fitowa daga taron, Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa batun kasafta kudaden watan Yuni ba ya ma cikin ajandar taron na su na yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel