Tsare-tsaren gwamnatin Buhari zai rika samar da ayyuka miliyan 3.7 a kowace shekara – Minista

Tsare-tsaren gwamnatin Buhari zai rika samar da ayyuka miliyan 3.7 a kowace shekara – Minista

Ministan Harkokin Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Okechukwu Enelamah, ya sanar da cewa manufar Farfado da Tattalin Arzikin Kasa da aka shigo da shi, zai rika samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya miliyan 3.7 a duk shekara.

A cewarsa wadannan ayyuka za su samar da zuba jari a kayayyakin jin dadin rayuwa da masana’antu, wanda hakan zai kara samar da ayyukan yi ga jama’a.

Enelamah ya ce an fi maida kai wajen samar da aikin ne ga matasa domin tabbatar da cewa su din ne suka ci moriyar wannan shiri.

Ya ce daga nan zuwa 2020 ana sa ran samar da ayyuka ga matasa har miliyan goma sha biyar.

Tsare-tsaren gwamnatin Buhari zai rika samar da ayyuka miliyan 3.7 a kowace shekara – Minista

Tsare-tsaren gwamnatin Buhari zai rika samar da ayyuka miliyan 3.7 a kowace shekara – Minista

An dai gudanar da wannan taro na hadin kai da wata kungiyar da ke kasar Amurka tare da hadin gwiwa da Gidauniyar Citi Foundation a babban tarayya Abuja.

KU KARANTA KUMA: Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

A cikin watan Afrilu, 2017 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a bisa kudirin nan da 2020 zai samar da ingantaccen tattalin arzikin kasa a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel