Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa a APC

Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa a APC

- Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewar shine jama’a zasu zaba a matsayin gwamnan jihar Enugu a zabe mai zuwa

- Jarumin Fim din ya bayyana cewar zai yi takarar na karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasa duk da kasancewar jam’iyyar PDP ce mai mulki a jihar Enugu

- Tun a watan Mayu jarumin ya bayyana cewar zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Enugu tare da bayyana cewar yanada da goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewar shine jama’a zasu zaba a matsayin gwamnan jihar Enugu a zabe mai zuwa.

Okonkwo, mai shirya fina-finai, mai da’awar kiristanci kuma lauya, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin day a fitar da wasu hotunansa na takara.

Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa a APC

Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa a APC

Jarumin Fim din ya bayyana cewar zai yi takarar na karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasa duk da kasancewar jam’iyyar PDP ce mai mulki a jihar Enugu.

A jikin hotunansa na takara, Okonkwo, ya rubuta cewar “A hannun Allah nake nema domin idan ya amince min babu wanda zai hana ni zama gwamna,” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta, Instagram.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Al'umma a jihar Kano sun yi barazanar kauracewa zaben 2019

Tun a watan Mayu jarumin ya bayyana cewar zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Enugu tare da bayyana cewar yanada da goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime.

Okonkwo y ace zai yi amfani da kujerarsa ta gwamna domin inganta harkokin shirya fina-finan masana’antar Nollywood, ta ‘yan kudancin Najeriya.

Kafin a ga matakin takara, jarumin na bukatar lashe zaben cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel