N5, 000 nake karba a duk harin kunar bakin wake da na dauki nauyin shirya

N5, 000 nake karba a duk harin kunar bakin wake da na dauki nauyin shirya

Wani mutum mai halitta irin ta wadanni, Abubakar Kori mai gudanar da al'amurran harin bamai-bamai na Boko Haram ya bayyana cewa, baya samun kasa da Naira dubu biyar a duk harin bam na kunar bakin wake da ya shirya a garin Maiduguri.

Kori mai shekaru 25 a duniya na daya daga cikin 'yan ta'adda 22 da hukumar 'yan sanda ta cafke a jihar Borno da Yobe da ake zargin hannun su cikin hare-haren kunar bakin wake da 'yan ta'dda na Boko Haram ke faman aiwatar wa a kasar nan.

Wannan wada ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa, ya na karbar kudin aiki na N5, 000 a kowane harin bam na kunar bakin wake da ya samu nasarar shiryawa a birnin Maiduguri da kewaye.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kori ya kasance mai gadi a wani gidan mai dake yankin Dalori a birnin Maiduguri, inda ya bayyana cewa akwai sa hannun sa cikin mafi akasarin harin bama-bamai na kunar bakin wake da suka afku a kwana-kwanan nan cikin birnin na Maiduguri.

N5, 000 nake karba a duk harin kunar bakin wake da na dauki nauyin shirya

N5, 000 nake karba a duk harin kunar bakin wake da na dauki nauyin shirya

Legit.ng ta fahimci cewa, aikin wannan matashi shine tabbatar da isar sakonnin bama-bamai ga wadanda zasu aiwatar da harin.

A nasa bangaren, wani dan ta'adda Adam Mustapha mai inkiyar Ba'Adam ya bayyana cewa, ya shirya hare-haren kunar bakin wake da dama da suka yi sanadiyar salwantar rayukan daruruwan mutane a garin na Maiduguri.

Ba'Adam mai shekaru 20 ya fayyace yadda ya shirya gudanar da wasu hare-haren kunar bakin wake a Bulukuntu, Baga, Garejin Muna da wasu yankuna daban-daban a birnin Maiduguri, inda ya karbi kudin aiki har na N200, 000 a karo biyu.

KARANTA KUMA: Ka yiwa doka biyayya akan Dasuki - Falana ya gargadi Shugaba Buhari

Yayin da manema labarai suka tuntube sa ko yana da na sanin wannan ayyuka da ya aiwatar, Ba'Adam ya bayyana cewa ko kadan babu alamar hakan a tattare da shi.

Wani dan ta'addan Ibrahim Mala mai shekaru 48, ya amsa laifin sa na taimakon aiwatar da wasu hare-hare kunar bakin wake a lokuta daban-daban a birnin Maiduguri, tare da sato shanu da ababen more rayuwa domin amfani ga 'yan ta'addan.

A nasa jawaban, babban jami'in dan sanda DCP Abba Kyari ya bayyana cewa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar cafke wannan 'yan ta'adda ne a wasu sassa daban-daban cikin yankunan Borno da Yobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel