Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

Zababben gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya bayyana kudirinsa na bincikar ayyukan gwamna mai barin gado Ayodele Fayose idan ya karbi mulki a hannunsa nan da yan watanni.

Da yake Magana da manema labarai a majalisa bayan ziyarar da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja a ranarAlhamis, 19 ga watan Yuli, ya bayyana cewa rashin tunani ne idan har ana ganin zai daukje idanu kan abubuwan baya.

Kan rahotanni dake yawo cewa sun siya kuri’u a lokacin zaben gwamnan jihar Ekiti da aka kammala kwanan nan, Fayemi yace baida masaniya akan haka saboda bai ga makamancin haka ba a wuraren da ya ziyarta.

Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

Zan binciki gwamnatin Fayose – Fayemi

Ya jadadda cewa buri sa a kullun shine ganin ci gaba mutanensa ta hanyar inganta rayuwarsu da ababen more rayuwa.

A halin da ake ciki, Hukumar zaben mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa zaben gwamna da aka kammala a karshen mako na jihar Ekiti ya kasance cikin gaskiya da aminci.

KU KARANTA KUMA: Kashe kashe: Sheikh Bala Lau ya yi kira da a tashi tsaye da addu'o'i

Hukumar zaben ta bayyana hakan a ranar Laraba a karshen ganawar da akayi tsakanin shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu da kwamishinonin zabe na yankuna (REC) a fadin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel