Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade uku a ma'ikatun gwamnatin tarayya

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade uku a ma'ikatun gwamnatin tarayya

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin wasu manyan direktocin wasu cibiyoyi uku a karkashin ma'aikatan Ma'adinai da Karafa.

Babban sakateren ayyuka na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Olusegun Adekunle, ne ya bayar da bayyana hakan cikin wata sanarwa a ya aike wa Premium Times a yau Alhamis.

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade uku a ma'ikatun gwamnatin tarayya

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade uku a ma'ikatun gwamnatin tarayya

DUBA WANNAN: Badakalar N500m: Kotu ta amince da bukatar bayar da belin wasu jiga-jigan 'yan PDP da aka gurfanar

Wadanda aka nada sune:

1) Injiniya Umar Albarka Hassan a matsayin shugaban na cibiyar hakar ma'adinai da karafa (NSRMEA) dake Kaduna.

2) Farfesa (Injiniya) Suleiman Bolaji Hassan a matsayin shugaban Cibiyar binciken hakar ma'adinai da kimiyya duwatsu dake Jos.

3) Farfesa (Injiniya) Linus Okon Asuquo a matsayin shugaban Cibiyar habbaka fasahar karafa dake Jos.

Dukkansu zasu fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Yulin 2018 kuma zasu kasance a matsayinsu har na wa'addin shekaru hudu.

"Shugaban kasar ya horesu da suyi amfani da kwarewarsu da sanin makamashin aiki wajen farfadowa da inganta cibiyoyin da aka damka a hannayensu.," Kamar yadda Mr. Adekunle ya fadi.

Ya kuma bukaci su dage wajen gudanar da ayyukansu saboda muhimmancin da sashin ma'adanai yake dashi a tsarin gwamnatin tarayya na mayar da fanin karafa da ma'adinai cikin manyan fanin da zasu habbaka tattalin arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel