PDP ta yi Allah-wadai da kona makarantar da sanata Dino Melaye ya gina

PDP ta yi Allah-wadai da kona makarantar da sanata Dino Melaye ya gina

- Dino Melaye na cigaba da amsar gaisuwar dannar kirji bayan 'yan barandar siyasa sun bankawa makarantar da ya gina wuta

- Jam'iyyar PDP ce nan ma tayi nata jawabin kan kona gine-ginen biyu

A ranar Larabar nan ne jamiyyar PDP reshen jihar Kogi su kayi Allah wadai da konewa tare da lalata wasu makarantu guda biyu da Sanata Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma ya gina su a matsayin aiyukan mazabunsa.

PDP ta yi Allah-wadai da kona makarantar da sanata Dino Melaye ya gina

PDP ta yi Allah-wadai da kona makarantar da sanata Dino Melaye ya gina

Cikin wata sanarwa da daraktan bincike da adana muhimman bayani na jamiyyar Achadu Dickson ya bayyana, inda ya ce matakin da ‘yan zambar siyasa suka dauka na cinna wuta da kuma lalata makarantu abu ne da samsam bai dace ba.

KU KARANTA: Da dumin sa: Jam'iyyar PDP tayi barzanar kin shiga zabukan 2019

Sanarwar ta kara da cewa wannan al'amari na a matsayin wata babbar hasara ga al'ummar jihar Kogi domin kuwa ba sanata Dino Melaye ne ya yi hasara ba. Sannan jamiyyar ta yi kira ga jami'an tsaro da su yi kokarin gano wadanda su ka aikata wannan danyan aikin.

A karshe jamiyyar PDP ta jajantawa iyaye da daliban jihar akan al'amarin da ya faru tare kuma da jan hankalin matasa da su kauracewa shiga bangar siyasa domin su ne shuwagabannin gobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel