Hukumar NSCDC ta samar da kudaden shiga na N4m a Jihar Oyo

Hukumar NSCDC ta samar da kudaden shiga na N4m a Jihar Oyo

Hukumar NSCDC (Nigeria Security and Civil Defence Corps) reshen jihar Oyo, ta samar da Naira miliyan 4 na kudaden shiga ta hanyar yiwa jami'an tsaro masu zaman kansu rajista a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2018.

Kakakin hukumar reshen jihar, Mista Olusegun Oluwole, shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Ibadan.

Oluwole yake cewa, cikin watanni bakwan da suka gabata hukumar ta kuma samu nasarar kwakulo Naira miliyan 26.8 daga hannun mazambata inda tuni ta mayarwa da mamallakan wannan dukiya.

Hukumar NSCDC ta samar da kudaden shiga na N4m a Jihar Oyo

Hukumar NSCDC ta samar da kudaden shiga na N4m a Jihar Oyo

A halin yanzu akwai kimanin kamfanoni 731 na jami'an tsaro masu zaman kansu dake ci gaba da gudanar da al'amurransu a fadin jihar inda hukumar ke horas da wasun su a rukunin ta.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta amince kan biyan tallafin N348bn ga 'Yan Kasuwar man Fetur

Oluwole ya ci gaba da cewa, shugaban hukumar reshen jihar, John Adewoye, ya sha alwashin daukar mataki kan duk wasu kamfanoni masu zaman kansu na jami'an tsaro dake gudanar da al'amurransu ba bisa ka'ida ba cikin jihar.

A yayin haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ta dakume wasu direbobi biyu na tankar mota makire da Lita 66,000 na man fetur yayin da suka yi yunkurin arcewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel