Da dumin sa: Jam'iyyar PDP tayi barzanar kin shiga zabukan 2019

Da dumin sa: Jam'iyyar PDP tayi barzanar kin shiga zabukan 2019

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP), ta yi barazanar kin shiga tare da janye jikin ta daga dukkan zabukan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC a shekarar 2019 idan dai har suka ga alamar ba za'a yi masu adalci ba.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa ne dai Prince Uche Secondus ya ayyana hakan a ranar Alhamis da yamma lokacin da yake karbar bakuncin wata tawagar hadin gwwiwa ta wasu kungiyoyin rajin tabbatar da demokradiyya a ofisin sa.

Da dumin sa: Jam'iyyar PDP tayi barzanar kin shiga zabukan 2019

Da dumin sa: Jam'iyyar PDP tayi barzanar kin shiga zabukan 2019

KU KARANTA: Jerin sunayen attajiran Afrika na 2018

Legit.ng dai ta samu cewa kungiyoyin da suka kai masa ziyarar sun hada da International Republican Institute (IRI) da kuma National Democratic Institute (NDI).

A cewar Mista Secondus, kawo yanzu dai kam su ba su da yakinin cewa hukumar zabe ba za ta yi masu magudi ba musamman ma dai idan akayi duba da yadda aka rika cin zarafin su a zaben jihar Ekiti da ya wakana.

A wani kebantancen labari kuma da majiyar mu ta kafar jaridar The Cable ta rubuta da ka iya zama wata babbar badakala, an gano fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo da kin biyan haraji a shekarar 2016.

Haka ma dai rahoton na The Cable ya ce suma 'yan majalisar tarayya a shekarar basu biya nasu kason na haraji ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel