Ka yiwa doka biyayya akan Dasuki - Falana ya gargadi Shugaba Buhari

Ka yiwa doka biyayya akan Dasuki - Falana ya gargadi Shugaba Buhari

Babban lauyan nan mai fafutikar kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya janyo hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya gaggauta sallamar Kanal Sambo Dasuki sakamakon cika sharuddan sa na beli da yayi.

Tsohon mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, ya cika sharuddan beli kamar yadda babbar kotun kungiyar kasashen Yammacin Afirka da kuma babbar kotun tarayya dake garin Abuja suka gindaya.

Cikin wata sanarwa, Falana ya gargadi shugaba Buhari akan yiwa doka biyayya sakamakon tabbacin da ya bai wa al'ummomin kasashen duniya da cewar nauyin gwamnatin tarayya ne da yi biyayya ga duk wata doka da kuma sharudda bayar da 'yanci ga duk wanda ya cancanta.

Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin shekaru biyu da suka gabata ne babbar kotun tarayya ta tuhumci Kanal Dasuki da laifin cin amanar ƙasa tare da zagon ƙasa na wawuson makudan dukiya.

Ka yiwa doka biyayya akan Dasuki - Falana ya gargadi Shugaba Buhari

Ka yiwa doka biyayya akan Dasuki - Falana ya gargadi Shugaba Buhari

Babban Lauya Falana ya kafa hujjoji ga shugaba Buhari dangane da kalaman sa yayin halartar bikin cikar shekaru 20 da kafuwar babbar kotun duniya da aka gudanar a birnin Hague na kasar Netherlands.

KARANTA KUMA: Hatsari ya salwantar da rayuwar wasu tagwaye bayan ziyarar Mahaifiyar su a jihar Ogun

Cikin hukuncin babbar kotun tarayya ta gudanar a makon da ya gabata ta bayyana cewa, ko kadan ba bu wani dalili ko hujja ta ci gaba da tsare tsohon Sojin baya ga cika sharuddan beli, inda ta nemi a gwamnatin tarayya ta biya sa diyyar Naira Miliyan 15 sakamakon rashin sukuni da ta jefa sa ciki.

Sai dai kawowa yanzu bayan tsawon lokuta na umarnin kotun, gwamnatin tarayya ta gaza wani kyakkyawan yunkuri domin sallamar tsohon sojin daga gidan kaso da za a ci gaba da gudanar da shari'ar sa a wasu lokuta na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel