Kashe kashe: Sheikh Bala Lau ya yi kira da a tashi tsaye da addu'o'i

Kashe kashe: Sheikh Bala Lau ya yi kira da a tashi tsaye da addu'o'i

Shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga Limamai, Malamai, dalibai da ma dukkan musulmai da su tashi tsayin daka da addu'o’i na neman Allah ya yaye mana fitintinun da ke addabar kasar Najeriya na kashe kashen Mutane.

Malamin wanda ya sanar da hakan a wani jawabi da ya fitar ta hannun kakakin sa, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman yace babu mafita da ya wuce addu'a a halin yanzu.

"Muna kira da ayi addu'a a dukkan majalisun ilimi, da makarantun islamiyoyi na yara da mata da manya, ayi addu'o'i da alqunut a dukkan salloli biyar.

Kashe kashe: Sheikh Bala Lau ya yi kira da a tashi tsaye da addu'o'i

Kashe kashe: Sheikh Bala Lau ya yi kira da a tashi tsaye da addu'o'i

"Sannan Limaman masallatan Juma'a ma suyi addu'a a lokacin khudubar Juma'a." cewar sa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC

Babban malamin ya kara da cewa lura da fitintinu da suka kunno kai a mafi yawan jihohin arewacin kasar, yace al'umma su koma ga Allah su nemi afuwa kuma su nemi Allah Ya yaye wannan bala'i.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel