Badakalar NYSC: Yarbawa sun bayyana cewa sharri wasu su ka shiryawa Ministar Buhari

Badakalar NYSC: Yarbawa sun bayyana cewa sharri wasu su ka shiryawa Ministar Buhari

- Wasu Yarbawa sun fito sun soki masu zargin Ministar kudi

- Ana zargin Minista Adeosun da amfani da satifiket din bogi

- Yarbawa sun ce ba za su yarda a rika taba Ministar kasar ba

Mun samu labari cewa wata Kungiya mai suna ODI Oduduwa Development Initiatives sun fito sun kare Ministar kudin wanda ake zargin ta kirkiri shaidar bogi na shirin bautar kasa NYSC. Yarbawan sun ce ba za su yarda da wannan cin fuska ba.

Badakalar NYSC: Yarbawa sun bayyana cewa sharri wasu su ka shiryawa Ministar Buhari

Wasu Yarbawa sun ce ana nema ayi masu cin kashi a Najeriya

Olusasumbo Akinleye wanda shi ne Shugaban wannan Kungiya ya bayyana cewa da gan-gan aka shiryawa Kemi Adeosun sharri domin kurum a bata mata suna da mutunci a gaban Jama’a. Akinleye yace ba za su yarda da wannan ba.

KU KARANTA: Wani babban Ma’aikacin NYSC ya tona asirin Ministar Buhari

Shugaban Kungiyar ta Oduduwa Development Initiatives ya bayyana cewa wasu ne saboda kabilanci su ka taso Ministar a gaba domin kuwa ta tare barnar da su ke yi. Kungiyar tace Ministar Bayarabiyace ‘Yar gidan mutunci da kima da daraja.

Kungiyar ta ODI ta kara da cewa kowa ya san irin kokarin da Ministar tayi na rike tattalin arzikin kasar nan a lokacin da abubuwa su ka tabarbare. Kungiyar tace ta lura da duk abin da ke faruwa kuma ta fahimci cewa sharri ake yi wa Ministar.

Dama kun san cewa wasu tuni sun fara kira a tsige Ministar kudin daga mukamin ta. Ta dai kai Shugaba Buhari ya ba Hukumar NYSC umarni ta binciki zargin da ke kan wuyar Ministar ta sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel