Badakalar N500m: Kotu ta amince da bukatar bayar da belin wasu jiga-jigan 'yan PDP da aka gurfanar

Badakalar N500m: Kotu ta amince da bukatar bayar da belin wasu jiga-jigan 'yan PDP da aka gurfanar

A yau Alhamis 19 ga watan Yuli ne wata babban kotun tarayya dake Legas ta bayar da belin wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP, Clement Faboyede da Modupe Adetokunbo a kan kudi N50 miliyan kowanensu.

Hukumar EFCC na tuhumar Faboyede, wanda shine Ciyaman din PDP na jihar Ondo da laifin karkatar da kudin al'umma wanda adadin ta ya kai N500 miliyan.

EFCC ta gurfanar da Faboyede ne a ranar 29 ga watan Yuni tare da Adetokunbo, wanda shine Direkta-Janar na yaki neman zaben jam'iyyar PDP a jihar lokacin zaben shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

Ana tuhumar su da aikata laifuka guda uku wanda suke da alaka fa karkatar da kudaden amma har yanzu sun ce basu aikata wannan laifin ba.

Badakalar N500m: Kotu ta amince da bukatar bayar da belin wasu jiga-jigan 'yan PDP da aka gurfanar

Badakalar N500m: Kotu ta amince da bukatar bayar da belin wasu jiga-jigan 'yan PDP da aka gurfanar
Source: Twitter

A ranar 10 ga watan Yuli, lauya mai kare wanda ake tuhuma, Mr. Eyitayo Jegede (SAN) da kuma lauya mai shigar da kara, Mr. Ekene Ihenacho sun tafka mahawara kan batun bayar da belin inda lauya mai shigar da kara ya nemi kotu ta hana belin.

A yayin da yake zartar da hukuncinsa, Alkali Muslim Hassan, ya lissafo dalilan da ya sa ya amince da bayar da belin wanda suka hada da yanayin laifin da ake tuhumarsu da aikatawa, irin hukuncin da za'a iya zartarwa da kuma yiwuwar wanda ake tuhumar zasu cigaba da aikata wani laifin.

Alkalin dai ya yanke hukuncin cewa sun cancanta a bayar da belinsu, kuma daga nan ne ya bukaci kowannensu ya bayar da N50 miliyan na belin tare da gabatar da mutanen da zasu tsaya musu.

Kotun tace duk wanda zai tsaya musu jingina sai ya kasance ma'aikacin gwamnatin jiha ko tarayya wanda matsayinsa na aiki baiyi kasa da mataki na 15 ba kuma ya kasance yana da gida a garin da kotun take.

An dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Satumban wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel