Zan sake gina Ajujuwan da aka kona a Lokoja, ba zan karaya ba – Sanata Dino Melaye

Zan sake gina Ajujuwan da aka kona a Lokoja, ba zan karaya ba – Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye yayi Allah wadai da wadanda suka kona ajujuwan da ya gina wa dalibai a makarantar Sakandare dake yankin mazabarsa na sarkin Noma, Lokoja, babban birnin jhar Kogi.

A ranar Laraba 18 ga watan Yuli ne aka ga cewa wasu yan iska sun kona ajujuwan da Dino ya gina sannan ake shirin kaddaarwa a a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli kurumus.

Melaye ya gina ajujuwan guda biyu ne a Makarantar Sakandare ta Sarkin Noma, da ke Lokoja.

Zan sake gina Ajujuwan da aka kona a Lokoja, ba zan karaya ba – Sanata Dino Melaye

Zan sake gina Ajujuwan da aka kona a Lokoja, ba zan karaya ba – Sanata Dino Melaye

Melaye ya ce bai ga dalilin da zai sa a dauki wasu abubuwan a maida su siyasa ba domin kuwa wannan bai kamata ba ko kadan.

KU KARANTA KUMA: Rade-radin sauya sheka: Gwamna Ortom ya isa hedkwatar APC domin ganawa mai muhimmanci tare da shugabannin jam’iyyar

Dino ya ce babu abin da zai hana shi ci gaban da rangadin mazabar sa da kaddamar da ayyuka sama da 100 da yayi musu cikin shekara uku da suka tura shi majalisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel