Ana gudu ana susar kuturi: APC ta fatattakii wani dan majalisa akan cin amanar jam’iyya

Ana gudu ana susar kuturi: APC ta fatattakii wani dan majalisa akan cin amanar jam’iyya

Uwar jam’iyyar APC reshen jihar Edo a mazabar Uhonmora 2 ta ladaftar da wani dan majalisar dokokin jihar Edo bisa zarginsa da cin amanar jam’iyyar ta hanyar yin ayyukan dake cin dunduniyar jam’yyar.

Shugaban APC a mazabar, Lucky Aroye ya tabbatar da dakatar da dan majalisa Ojo Asein a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli, inda yace tuni sun sanar da shugabancin jam’iyyar a matakin karamar hukuma da na jaha, game da sallamar Ojo.

KU KARANTA: Duk irin mukamin da Buhari zai baiwa Rarara ba zai tara abinda na tara ba – Inji Nazir Ahmad

Aroye ya bayyana cewa sun kama Ojo da laifin cin amanar APC ta hanyar gudanar da wasu tarukan sirri da yayan jam’iyyar adawa ta PDP, inda yake shaida musu cewa nan bada jimawa ba zai sheke zuwa PDP. Haka zalika sun zarge shi da harzuka magoya bayansa game da matakin da jam’iyyar ta dauka akansa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aroye yana cewa: “Asein ya sha fada ma magoya bayansa cewa su shirya don a kowanni lokaci zasu fice daga APC zuwa PDP, mun sha gargadinsa, amma yaki ji, don haka ne muka sanar da karamar hukuma da jihar matakin da zamu dauka akansa.”

Sai dai da kamfanin dillancin labaru, NAN, ta tuntubi dan majalisa Ojo ta wayar tarho don jin ta bakinsa game da lamarin, sai yace “babu abinda zan ce game da wannan mataki da suka dauka, amma babu wanda ya isa ya sallameni daga jam’iyyar nan.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel