Rahoto: Yan matan Chibok dake hannun Boko Haram basu son dawowa – Abba Kyari

Rahoto: Yan matan Chibok dake hannun Boko Haram basu son dawowa – Abba Kyari

Rahoto ya nuna cewa sauran ‘yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram basu son dawowa daga wajen iyayensu.

Yayinda an ceci 163 daga cikinsu, sauran guda 100 da suka rage a hannun yan tada kayar bayan Boko Haram.

Hukumar yan sanda a ranan Laraba sun bayyana mutane takwas da ke da hannu cikin garkuwa da yan matan Chibok 276 a makarantan Sakandaren Chibok a jihar Borno a shekarar 2014.

Hazikin hafsan yan sanda, Abba Kyari, ya bayyanawa CNN cewa Mayinta Modu, babban kwamandan Boko Haram wanda ya shirya yadda aka sace yan matan ya fada musucewa an aurar da sauran yan matan kuma basu da niyyar dawowa gida.

KU KARANTA: Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin BuharI

Game da cewar Modu, yan matan sun karbi akidar Boko Haram kuma basu ga dalilin da zai sa su dawo gida ba.

Abba Kyari yace: “Sun ce yawancin yan matan sun karbi akiidar Boko Haram kuma basu ga dalilin da yasa za su bar mazajensu ba. Wadanda suke son dawowa ne aka saki a yarjejeniyar da akayi,”

“Sun bayyana cewa suna cikin wadanda sukayi garkuwa da yan matan Chibok. Daya daga cikinsu wanda kwamanda ne ya ce su kusan 100 ne suke aiwatar da wannan aiki.”

Ahmad Sakilda, danjarida wanda ya shahara da dauko rahoto daga Boko Haram ya bayyana a kwanakin baya cewa matan Chibok 30 kawai suka rage.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel