Yanzu Yanzu: Majalisa ya kaure da hayaniya yayinda sanatocin kudu maso gabas suka zargi Buhari da son kai

Yanzu Yanzu: Majalisa ya kaure da hayaniya yayinda sanatocin kudu maso gabas suka zargi Buhari da son kai

Zauren majalisa ya kaure da hayaniya na kimanin sa’o’i 30 bayan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya karanto wasikar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake neman yan majalisa su tabbatar da wasu nade-nade a hukumar kula da agajin gaggawa na kan hanya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ya tada jijiyar wuya akan cewa akwai bangaranci wajen nada shugabannin hukumomin gwamnati.

A cewarsa, nade-naden baya-bayan nan da shugaba Buhari yayi da kuma wadda yake neman amincewar majalisa ya nuna cewa wadanda aka zaba duk yan yankin kasar guda ne.

Shugaban masu rinjaye, Ahmad Lawan, ya yi jayayya kan cewa nade-naden yayi daidai “idan akayi duba ta fuskanci masu yawa.”

Yanzu Yanzu: Majalisa ya kaure da hayaniya yayinda sanatocin kudu maso gabas suka zari Buhari da son kai

Yanzu Yanzu: Majalisa ya kaure da hayaniya yayinda sanatocin kudu maso gabas suka zari Buhari da son kai

Saraki ya bayyana cewa majalisa ba za ta yi la’akari da kabilanci da ra’ayi ba, inda yace kwamitin lamuran tarayya ta binciki nade-naden Buhari sannan gabatar da rahoto a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nada tsohon mataimakin gwamnan CBN, Lemo a matsayin shugaban FERMA

Don haka sai hayaniya ya kaure a zangon majalisan, inda yan majalisa ke ihun ‘eh’da ‘a’a’.

Baya ga Ekwaeremad, yan majalisa ku daga kudu maso gabas sun bukaci majalisa da ta dakatar da cigaba da tantance wadanda aka gabatar har zuwa lokaci da kwamitin ta gaatar da rahoton ta.

Sanatocin da suka tada jijiyoyin wuyan sun hada da Chukwuka Utazi, Mao Ohuabunwa da kuma Obinna Ogba‎.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel