Karanta kaji kuskure 1 da ya jawo tonuwar asirin wani mai garkuwa da mutane

Karanta kaji kuskure 1 da ya jawo tonuwar asirin wani mai garkuwa da mutane

- Rashin godiyar abinda ya samu bayan karbar kudin fansa har Naira miliyan daya ya kawo karshen mummunar sana'ar garkuwa da mutanen da yake yi

- Tuni dai 'yan sanda suka cafke shi kuma har suna shirin gurfanar da shi gaban alkali da zarar sun kammala bincike

Wani mai garkuwa da mutane mai suna Sunday Okoli ya shiga komar jami'an tsaro a lokacin da yake kokarin karbar cikon ragowar kudin fansar da ya bukata, kimanin Naira 300,000.

An kama mai garkuwa da mutane a lokacin da yake kokarin karbar ragowar kudin fansar da ya nema

An kama mai garkuwa da mutane a lokacin da yake kokarin karbar ragowar kudin fansar da ya nema

Tun da farko dai mai garkuwa da mutanen ya karbi kudi kimanin Naira miliyan daya a matsayin kudin fansar garkuwa da yayi da wasu ‘yan wasan kwaikwayo masu suna Ugo Stevenson da kuma Izunna Obiakor, mazauna garin Oweri da ke jihar Imo.

KU KARANTA: Barawon da ya tsare daga wurin ‘yan sada ya sake shiga hannu

Mai garkuwa da mutanen ya sako mutanen biyu ne, bayan shafe kwana biyar a gurinsa, inda su ka biya Naira miliyan daya, amma sai ya rike motar daya daga cikinsu kirar Toyota ya sale bukaci Naira 300,000 Kafin ya basu motar.

Bayan da ya bukaci wannan adadin kudin, sai aka hada baki da jami'an rundunar ‘yan sanda na SARS, su kuma su ka damke shi a lokacin da ya zo karbar cikon kudin.

A karshe jami'an tsaron sun bayyana cewa Sunday yana tsare hannunsu domin zurfafa bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel