Yanzu-yanzu: Osinbajo, gwamnoni, shugaban NNPC, gwamnan CBN, sun shiga ganawar gaggawa

Yanzu-yanzu: Osinbajo, gwamnoni, shugaban NNPC, gwamnan CBN, sun shiga ganawar gaggawa

Mataimakin shugabna kasa, Yemi Osinbajo, wasu gwamnonin Najeriya sun shiga ganawar kwamitin tattalin arzikin Najeriya a fadar shugaban kasa, Aso Villa Abuja.

An kaddamar da wannan ganawa ne misalin karfe 11:10 na safiyar nan tare da gwamnonin jihar Katsina, Sokoto, Kebbi, da wasu mataimakan gwamnonin jihohin tarayya.

Wadanda ke hallare cikin manyan jami’an gwamnati sune gwamnan babban bankin tarayya CBN, Godwin Emefiele; shugaban kamfanin man feturin Najeriya, Maikantai Kachalla Baru da sauran su.

A karshen ganawar, za su bayyanawa manema labarai abinda suka tattauna.

KU KARANTA: Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Za ku tuna cewa kwamitin gwamnonin Najeriya a ranan Laraba sun gana a Abuja domin tattaunawa kan kudin da gwamnatin tarayya da ke basu kowani amma basu samu a watan Yuni ba.

A karshen watan Yuni, anyi baran-baran a zaman da akayi saboda ana zargin NNPC ba su biyan gwamnati kudin da ya kamata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel