Boko Haram sun dawo tare tituna, sun kar mutane daren jiya a hanyar Dikwa

Boko Haram sun dawo tare tituna, sun kar mutane daren jiya a hanyar Dikwa

Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayyukansu sakamakon harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai yayin da suka tare matafiya a babban titin Borno a ranar Talata.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan ta'addan sun tare matafiyan ne a tsakanin Ramin Aljanu da Logumani da hanyar kauyen Musane dake babban titin zuwa Dikwa/Ngala.

Sun kashe fasinjoji da dama bayan sun tare su. Sun kuma kona motoccin dake dauke da fasinjojin.

Boko Haram sun dawo tare tituna, sun kar mutane daren jiya a hanyar Dikwa
Boko Haram sun dawo tare tituna, sun kar mutane daren jiya a hanyar Dikwa

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku yadda 'yan bindiga suka kai hari wasu kauyukka a jihar Zamfara inda suka hallaka mutane sama da 30.

Ku biyo mu don samun karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164