Ko kun san yanda majalisar dattawa ta raba kujerun sanatocin da suka mutu

Ko kun san yanda majalisar dattawa ta raba kujerun sanatocin da suka mutu

- Zamu sake gudanar da zabe kafin nan da kwanaki 30 don cike guraben

- Cikin kujerun har da ta Joshua Dariye wanda aka yankewa shekaru 14 a gidan yari

Ko kun san yanda majalisar dattawa ta raba kujerun sanatocin da suka mutu

Ko kun san yanda majalisar dattawa ta raba kujerun sanatocin da suka mutu

Majalisar dattijai ta fitar da wasu kujeru a majalisar wanda babu kowa, cikin kujerun akwai ta Sanata Mustapha Bukar wanda ke wakiltar Katsina wanda ya rasu a ranar 4 ga watan Afrilu 2018 da kuma Ali Wakili na jahar Bauchi wanda shima ya rasu a ranar 17 ga watan Mayu 2018.

Cikin kujerun dai akwai ta Sanata Joshua Dariye wanda ke wakiltar jahar Plateau biyo bayan yanke masa zaman shekaru 14 a gidan kaso.

DUBA WANNAN: Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha

A ranar Laraba ne Ciyaman na INEC Prof Mahmoud Yakubu ya bayyana cewa akwai kujerar Marigayi Umar Jibril na Kogi wadda itama babu kowa akai.

Yakubu yace za'a gudanar da zaben nan da kwanaki 30.

Ya kara da cewa "A kwanakin bayane hukumar ta samu takardar neman aiki daga majalisar dangane da jahar Bauchi, Kogi,da Katsina.

"Duba da sha'anin doka hukumar zaben zata gudanar da shi nan da kwanaki 30,sannan zamu gudanar da zaben a ranar daya a dukkanni jahohin.

Da yake ganawa da wakilin mu Prof Itse Sagay (SAN) yace idan har zuwa yanzu Dariye yana ci gamba da karbar albashi to wannan ba daidai bane bayan yana gidan kaso.

Sagay yace" Bana tunanin har yanzu Dariye yana karbar albashi saboda hakan laifi ne a dokar mu. Duk wanda ya kasance a gidan kaso a dalilin zamba to bashi da albashi musamman wanda yake a majalisar dattijai".

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel