Majalisar Dattawa ta amince kan biyan tallafin N348bn ga 'Yan Kasuwar man Fetur

Majalisar Dattawa ta amince kan biyan tallafin N348bn ga 'Yan Kasuwar man Fetur

Majalisar Dattawa ta bayar da amincewar ta dangane da biyan tallafi na kimanin Naira Biliyan 348 ga kamfanonin 'yan kasuwar man fetur kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, majalisar ta bayar da wannan aminci ne yayin zaman ta da ta gudanar a ranar Larabar da ta gabata bayan nazari akan binciken kwamitin ta kan harkokin man fetur.

Yayin bayar da sahalewar biyan wannan makudan kudi kamar yadda majalisar ta gudanar, akwai kimanin 'yan kasuwa da za a biya N275,750,415,108 yayin da wasu 'yan kasuwa 19 za su tashi da kaso 65 cikin 100 na basussukan su na kimanin N73,452,639,866 kafin majalisar ta kammala binciken ta.

Majalisar Dattawa ta amince kan biyan tallafin N348bn ga 'Yan Kasuwar man Fetur

Majalisar Dattawa ta amince kan biyan tallafin N348bn ga 'Yan Kasuwar man Fetur

Wasu daga cikin sanannun kamfanonin man fetur da za a biya cikakkun kudin su hadar da; Aiteo, Bovas, Capital Oil, Eternal, Folawiyo Energy, Hyden, Integrated Oil, Mobil Oil Nigeria, MRS, NIPCO, NNPC Retail, Obat Oil, Sahara Energy da kuma Total Nigeria.

Sauran sanannun kamfanonin da su tashi da wani kaso na kudaden su sun hadar da; Conoil, Forte Oil, Honeywell, IPMAN Investment, Matrix Energy da kuma Oando.

KARANTA KUMA: Amfani 6 na shan Ruwan ɗumi ga Lafiyar 'Dan Adam

Cikin sakamakon binciken da kwamitin majalisar ya gabatar da sanadin jagoran sa, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa, an samu nakasun daidaito cikin ikirarin basussukan tallafin man fetur da 'yan kasuwar da kuma ma'aikatar kudi ta gabatar.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya nemi sahalewar majalisar dangane da biyan basussukan tallafin man fetur tun a ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel