Muna da kwakkwarar shaidar magudin da aka yi a jihar Ekiti - PDP

Muna da kwakkwarar shaidar magudin da aka yi a jihar Ekiti - PDP

- NWC tace hukumar INEC tayi gaggawar gyara sakamakon zaben.

- A ranar Talata ne dai NWC sukayi wani zama a Abuja inda suka tattara duk wani bayanai na zaben da aka gudanar a jahar Ekiti.

Muna da kwakkwarar shaidar magudin da aka yi a jihar Ekiti - PDP

Muna da kwakkwarar shaidar magudin da aka yi a jihar Ekiti - PDP

A ranar Talatar ne dai NWC sukayi wani zama a Abuja inda suka sake duba duk wani abu daya shafi zaben gwamnoni na jihar Ekiti da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.

Bayan tattara duk wani bayanai da NWC tayi, ta tabbata cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta riga ta bawa Jam'iyar adawa ta APC nasara tun kafin a gudanar da zaben.

DUBA WANNAN: Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu

"Bayan dogon nazari da bincike da aka gudanar ta tabbata dan takarar jam'iyar PDP Prof Kolafo Olusola shine ya lashe zaben da aka gudanar a jihar Ekiti a 14 ga watan Yuli.

NWC ta umarci INEC data gaggauta gyara sakamakon zaben sannan

kuma ta nemi gafarar al'ummar jihar Ekiti, sannan su fara shirin tunkarar kotun saurare.

A ranar Lahadi ne dai hukumar ta bayyana cewa Dr Kayode Fayemi na jam'iyar APC ne ya lashe zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel