PDP ta kulla yarjejeniya da Saraki da wasu gwamnoni 3

PDP ta kulla yarjejeniya da Saraki da wasu gwamnoni 3

Manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jiya sun kama tsare-tsare don dawowar wasu daga cikin tsoffin mambobinta ciki harda shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnoni uku.

Wata majiya ta bayyana cewa batun komawar Gwamna Ortom jam’iyyar PDP bai kammala ba saboda wasu lamuran dake jam’iyyar reshen garin.

Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers na wajen a lokacin da shugabannin ke tsare-tsare kan manufofinsu a jiya, Laraba, 18 ga watan Yuli.

PDP ta kulla yarjejeniya da Saraki da wasu gwamnoni 3

PDP ta kulla yarjejeniya da Saraki da wasu gwamnoni 3

Gwamnonin uku da akayi nasara akan su a jiya sun hada da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, Samuel Ortom na jihar Benue da Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara. Zuwa yanzu ba’a san adadin yan majalisar dokoki da ke cikin yunkurin ba.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa PDP ta aika sammaci ga dukannin yan takarar PDP kan ziyarar ta’aziyya Sokoto kan kashe-kashen mutane 39 da yan fashi suka yi.

dukannin yan takarar shugabancin kasa sun je Sokoto ciki harda, Atiku Abubakar, Tanimu Turaki, Sule Lamido da Ibrahim Shekarau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel